- Advertisement -

Zaɓen 2023: Mawaƙi Muddassir Ƙasim ya haska wa ‘yan Arewa hanyar samun mafita

0

Zaɓen 2023: Mawaƙi Muddassir Ƙasim ya haska wa ‘yan Arewa hanyar samun mafita

Malam Mudassir Ƙasim

- Advertisement -

FITACCEN mawaƙi a masana’antar Kannywood, Malam Mudassir Ƙasim, ya yi kira ga ‘yan Arewa da kada su yi sakaci wajen sama wa Arewa mafita ta hanyar zaɓuɓɓukan da za a yi a shekara mai zuwa.

Ya ce wajibi ne kowa ya mallaki katin zaɓe domin samar da shugaban da zai taimaki yankin “ko daga wace jam’iyya ya ke.”

Mawaƙin ya bayyana haka ne a wani tsokaci da ya rubuta mai taken “Arewa Mu Na Tsaka-Mai-Wuya”, wanda ya tura wa mujallar Fim.

- Advertisement -

Mudassir ya fara tsokacin sa ne da bayyana cewa, “Arewa a zaɓen 2023 an bar kari tun ranar tubani.”

Ya ci gaba da cewa: “Da farko dai da yawan mu ‘yan Arewa gwiwar mu ta yi sanyi a kan makomar Nijeriya, musamman makomar Arewa a yau sakamakon raunin ingancin ‘yan takarkaru, musamman na jam’iyyu masu ƙarfi.

“Tabbas, ba ma shakkar Yarbawa wajen iya mulki da ‘international test’ wajen ayyukan gina ƙasa domin sun ƙware a kan wannan, amma babban abin tsoro da ƙalubale gare mu shi ne mu Arewa a yanzu manyan matsalolin mu uku ne:

- Advertisement -

1) rashin tsaro sakamakon da aka taɓo Fulanin da ɗaukar fansar su ba ya ƙarewa har abada;

2) rashin ilimin ƙananan yara da mata da matasa;

3) Kama hanyar durƙushewar harkokin noma da kasuwanci.”

- Advertisement -

A yayin da ya ke juyayi kan ƙalubalen da yankin ke fuskanta, Mudassir ya ce: “Tambayar a nan, mu da aka ba mu dama shekara takwas ba mu iya magance waɗannan matsaloli ba, sai dai ma ƙara haɓaka su mu ka yi, ta yaya waɗanda ake zargin cewa su na da hannu wajen waccan tsokanar Fulanin da aka yi kuma su ka ƙi bada damar yin burtali don shawo kan matsalar, su ne za su zo su magance mana matsalolin mu? Wallahi abin tabbas akwai ban-tsoro a Arewa!”

Ya yi nuni da cewa su kuma manyan Arewa, yanzu ba wannan matsalar ce su ka sa gaba ba, “kawai rikicin shugabanci ne a gaban su, ba yadda za a ceto Arewar ba.”

Mawaƙin ya ƙara da cewa babu wani tabbas da yaƙini a kan cewa duk ‘yan takarar nan da su ka fito daga yankuna daban-daban na ƙasar nan za su iya magance matsalar Arewa.

- Advertisement -

“Dama-dama wanda ya fito daga yankin Arewa-maso-yamma ma, domin akwai kyakkyawan zato a kan shi na kishin Arewa, amma kuma matsalar ita ce tuni ya yi wa Arewar baƙin cikin samun wannan hazaƙa tashi da ya je ya shiga ƙaramar jam’iyya da a wani yanki kawai ta ke, ba lallai ta iya mamaye ƙasar a wannan zango na zaɓe ba.”

Da ya koma kan inda za a samu mafita, Mudassir ya ce, “Ni ma kam kai na ya kulle a nan, domin har yanzu ba mu shirya kare kan mu daga yaudarar da ake mana ba. Mun ƙi fita mu yi rajistar katin zaɓe, kowa sai ka ji ya na cewa shi ya daina zaɓe.

“Shin ɗan’uwa idan ka daina fa? Ita ƙasar taka ba za ta daina don ka daina ba, za a zaɓa maka ko ka na so ko ba ka so. To gara ka fito ka yi katin zaɓe, mu yi rubdugu mu jefa ma wanda mu ke ganin zai ba mu mafita mai ma’ana a Arewa ko daga wace jam’iyya ya ke.

- Advertisement -

“Ƙuri’a ɗaya tak za ta canja mulkin kama-karya. Haka nan ƙuri’a ɗaya tak ke jawo kama-karya.

wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy