Zaɓen Fidda Gwani na APC: Ƴan Takara sun ziyarci Deliget a Otel
Zaɓen Fidda Gwani na APC: Ƴan Takara sun ziyarci Deliget a Otel
Gabanin Zaben Fidda Gwani na Shugaban Ƙasa na Jam’iyyar APC, manyan Ƴan Takara da suka haɗa da Bola Tinubu, da Yemi Osinbajo, da Rotimi Amaechi, da Kayode Fayemi, da Ahmad Lawan ta hanyar wakilan su, sun je wajen Deliget a ɗakunan, domin su nemi su zaɓe, kamar yadda Daily Trust ta bayyana.
APC.
An gano cewa, Deliget da suka zo daga Jahohin APC Gwamnatocin Jahohin su, sun basu masauki, inda waɗanda ba APC ke mulki ba, su kuma ƴan Takara sun basu wurin kwana.
Ɗan Majlisa wanda shine Jami’in wani Ɗan Takara yace sun bada wasu ƴan alawus ga Deliget domin su sayi abinci.
“Babu fara abun ba, amma mun fara ne ta kaɗan,” Inji shi.
Wata Majiyar tace Gwamnoni na zuwa wajen Deliget ɗin su.
