Za’a Kashe Naira Billiyan 8.3 Domin Sanarwa Yan Sanda Kayan Aiki, Da Walwala——Alhaji Mohammed Dingyadi

0

Za’a Kashe Naira Billiyan 8.3 Domin Sanarwa Yan Sanda Kayan Aiki, Da Walwala——Alhaji Mohammed Dingyadi - Dimokuradiyya

‘Majalisar zartaswa ta tarayya ta amince da Naira biliyan 8.3 don siyan motoci da kayan aiki ga rundunar ‘yan sandan Najeriya.

Ministan kula harkokin ‘yan sanda, Alhaji Mohammed Dingyadi ne ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata a lokacin da yake zantawa da manema labarai a fadar gwamnatin bayan taron majalisar FEC da mataimakin shugaban kasa Yemi Osinbajo ya jagoranta.

Dingyadi ya ce amincewar ta kuma shafi samar da magunguna da kayan aikin jinya ga asibitocin ‘yan sanda.

“A yau, Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da Asusun ‘Yan Sandan Nijeriya (NPTF) don bayar da kwangilar samar da motocin aiki guda 82, kirar Toyota, domin gudanar da aikin ‘yan sandan Nijeriya yadda ya kamata a kan kudi Naira biliyan 2.2.


Download Mp3

“Mun kuma samu amincewar samar da riguna na ‘yan sanda na musamman domin rabawa ‘yan sanda a fadin kasar nan kan kudi Naira biliyan 1.9.

“Haka kuma an waye akudi Naira miliyan 576 domin samar da Sabbin takalmar Yan sanda; Mun kuma samu amincewar samar da kananan kayan agajin gaggawa ga ‘yan sanda kan kudi Naira biliyan daya da kuma kayayyakin koyarwa na kwalejojin ‘yan sanda da makarantu a kan Naira miliyan 664.

“Har ila yau, akwai bukatar wadatar magunguna da kayan aikin jinya ga asibitocin ‘yan sanda a fadin kasar nan kan kudi naira biliyan biyu; idan aka hada wadannan ayyuka za su kai Naira biliyan 8.3,” inji shi.

Ministan ya bayyana cewa an kafa Asusun na NPTF ne a matsayin wani asusu na musamman domin saukaka inganta ayyukan rundunar ‘yan sandan Najeriya ta fannin kayan aiki, horo da kuma Samar da walwala.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy