- Advertisement -

Za’a yi ruwa kamar da bakin kwarya a wasu sassan kasar nan– NiMet

0

Za’a yi ruwa kamar da bakin kwarya a wasu sassan kasar nan– NiMet - Dimokuradiyya

Hukumar hasashen yanayi ta kasa NiMet ta yi hasashen zazzafar rana da ruwa kamar da bakin kwarya daga ranar Laraba zuwa Juma’a a fadin kasar nan.

- Advertisement -

Hasashen Yanayin NiMet da aka fitar a ranar Talata a Abuja ya yi hasashen sararin samaniya a ranar Laraba tare da tsaikon hasken rana a waus yankuna dake arewacin kasar nan da safe, tare da yiwuwar ruwa kamar da bakin kwarya a kan jihohin Kebbi, Zamfara, Kano da Kaduna.

Hukumar ta kuma yi hasashen samun ruwan sama a sassan Ebonyi da Abia da Imo da Ribas da Delta da kuma jihar Akwa Ibom da rana da yamma.

A cewar NiMet, ya kamata a gyara magudanar ruwa daga tarkacen da suka toshe su, don tabbatar da kwararar ruwa yadda ya kamata, don rage afkuwar zaizayar kasa da ambaliyar ruwa fiye da yadda aka saba gami a wasu sassan kasar nan.

- Advertisement -

A wani labarin kuma na daban

Yanzu-Yanzu: Dan majalisar jihar Oyo, Olusegun Popoola ya rasu

Dan majalisar dokokin jihar Oyo, Ademola Olusegun Popoola ya rasu.

- Advertisement -

DAILY POST ta tattaro cewa Popoola ya mutu ne da sanyin safiyar yau Laraba.

Dan majalisar dai yana wakiltar mazabar Ibadan ta kudu maso gabas II a majalisar dokokin jihar Oyo.

Wakilin majiyar jaridar Dimokiradiyya ya ruwaito cewa dan majalisar ya rasu ne a asibitin Kwalejin Jami’ar (UCH) Ibadan.

- Advertisement -

An zabi dan majalisar ne a shekarar 2019 domin wakiltar yankin a jam’iyyar PDP.
Rahotanni sun nuna cewa dan majalisar ya rasu ne bayan ya yi fama da cutar koda.

Ya rasu yana da shekaru 46 a duniya.

Kafin rasuwarsa Popoola shi ne Shugaban, Kwamitin Majalisa kan Al’amuran Kananan Hukumomi da Sarautun gargajiya.

- Advertisement -

Oyekunle Oyetunji, mai baiwa kakakin majalisar dokokin jihar shawara kan harkokin yada labarai, Adebo Ogundoyin, ne ya tabbatar da rasuwar dan majalisar a safiyar yau Laraba.

Ya ce, “Na’am. An tabbatar”.

- Advertisement -
wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy