- Advertisement -

Zaben 2023: Gwamnan Ganduje Ya Taya Kashim Shettima Murna, Bisa Zama abokin takarar Bola Tinubu

0

Zaben 2023: Gwamnan Ganduje Ya Taya Kashim Shettima Murna, Bisa Zama abokin takarar Bola Tinubu - Dimokuradiyya

Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya taya tsohon gwamnan jihar Borno Kashim Shettima murna bisa nasarar da ya samu ma zama mataimakin dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben dake tafe.

- Advertisement -

Gwamnan cikin sanarwar da aka rabawa manema labarai ta hannun kwamishinan yada labarai na jihar, Kwamared Muhammad Garba, ya bayyana Shettima a matsayin daya mai tamkar da babu iyaka.

A cewar Gwamnan Ganduje, Sanatan Shettima, bashi bukatar wani shiri don zama mataimakin shugaban kasa, don kuwa koda yaushe cancantar sa ta sanya ya zama a cikin cikakken shiri na ko ta kwana.

Ya kara da cewa lokacin da aka gudanar da zaben Fidda Gwanin dan takarar shugaban kasar, ya gana da Shettima dangane da batutuwan shugabanci, kuma anan ya sake gaskata kwarewar sa.

- Advertisement -

Gwamnan na Kano daga nan sai ya godewa Jagoran Jam’iyyar APCn, kuma ɗan takarar shugaban kasa a zaben dake tafe, bisa yadda yayi hangen nesa wajen zabo Shettima a matsayin mataimakinsa, da zasu yi takara tare.

A karshe Ganduje yayi kira ga yan kasar nan, musamman ya’yan jam’iyyar APC, kan suyi duk mai yiwuwa wajen ganin mutanen sun yi nasara a zaben baɗi, dama sauran madafun kasa baki daya.

- Advertisement -
wt11 gif

- Advertisement -

Get real time updates directly on you device, subscribe now.

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy