Zaben Ekiti: EFCC ta kama wani da zargin dan APC ne da siyan kuri’u

0

Yanzu-Yanzu: Zaben Ekiti: EFCC ta kama wani da zargin dan APC ne da siyan kuri’u - Dimokuradiyya

Jami’an Hukumar Yaki da yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati, EFCC, a ranar Asabar, sun kama wani da ake zargi da siyan kuri’u a jihar Ekiti a yayin da ake fara zaben gwamnan jihar.

Jami’an EFCC sun kama wanda ake zargin dauke da buhun kudi a yayin da ake “tantance masu zabe.”

Wanda ake zargin, wakilin jam’iyyar APC mai mulki ne, an tsare shi a makarantar Ola Oluwa Grammar School da ke kan titin Ilawe na garin Ekiti babban birnin jihar.


Download Mp3

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta gargadi masu kada kuri’a gabanin zaben kan siyan masu kada kuri’a.

INEC ta yi gargadin daukar tsauraran matakai kan bai wa masu kada kuri’a kudi.

Hukumar ta bayyana hakan ne a lokacin da take bayyana hadin gwiwarta da hukumomin yaki da cin hanci da rashawa ta EFCC da ICPC, a ranar Juma’a.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy