Zaben Gwamnan Osun: INEC zata dauki masu bukata ta musamman aikin zaben

0

Zaben Gwamnan Osun: INEC zata dauki masu bukata ta musamman aikin zaben - Dimokuradiyya

Kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta a jihar Osun, Farfesa Abdulganniy Rabi, yace zasu dauki masu bukata ta musamman domin aiki tare dasu.

Farfesa Raji yace masu bukatar ta musamman zasu kasance cikin rukunin Ma’aikatan wucin gadi da hukumar zata dauka, domin aikin zaben Gwamnan jihar da za a gudanar.

INEC dai ta shirya gudanar da zaben Gwamnan jihar Osun ne, ranar 16 ga watan Yuli Mai kamawa.


Download Mp3

Raji ya sanar da wannan albishirin ne lokacin da yake ganawa da shugaban kungiyar masu bukata ta musamman na sanatoriya jihar a Osogbo.

Ya kara da cewa wannan kokarin da zasu zai taimaka wajen shigar da masu bukata ta musamman cikin al’umma yadda ya kamata, tare da kawar musu da zargin kyamar su da suka tunani.

Da yake nasa jawabin daraktan cibiyar dimokuraɗiyya a Najeriya, Me Steven Snook, ya bukaci INEC ta tabbatar da cewa ta dauki masu bukata ta musamman din kamar yadda ta sanar.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy