Zamu Cigaba da Kare Ƴan Najeriya Mazauna Kasashen Waje — Buhari

0

Zamu Cigaba da Kare Ƴan Najeriya Mazauna Kasashen Waje — Buhari - Dimokuradiyya

Zamu Cigaba da Kare Ƴan Najeriya Mazauna Kasashen Waje — Buhari

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari a ranar Alhamis a Kasar Madrid, yace Gwamnatin Tarayya zata yi rige-rige wajen kare ƴan Najeriya mazauna Ƙasashen waje.


Download Mp3

Buhari ya bada umarnin a lokacin da ya gana da ƴan Najeriya mazauna Ƙasar Spain a ziyarar sa daya kai na kwanaki uku.

A cewar sanarwar da Mai bashi Shawara ta Fuskar Kafafen Yaɗa Labaru Femi Adesina, tawagar ƴan Najeriya wadda ta gana da Shugaba Buhari, daya haɗa da Shugaban Ƙungiyar John Bosco, Mataimakin sa Richard Omoregbe, Ɗan wasan Super Eagles da yake wasa a Spain a Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Madrid Kenneth Omeruo, da Obinna Okafor, da Dalibin koyan Sufurin Jirage Mohammed Bashir, da Segun Adedoyin, da Dan Kasuwa Bright Omorodion.

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya shaidawa ƴan Najeriya cewa sune Jakadun Ƙasar yace “da yawan ku kuna wannan ƙasa a dalilai daban-daban, musamman a wasanni inda kuke samun abun da kuke rayuwa.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy