Zamu magance Matsalar Tsaro, da Inganta Tattalin Arziki — Kwankwaso

0

Zamu magance Matsalar Tsaro, da Inganta Tattalin Arziki — Kwankwaso - Dimokuradiyya

Zamu magance Matsalar Tsaro, da Inganta Tattalin Arziki — Kwankwaso

Ɗan Takarar Shugaban Ƙasa a Jam’iyyar NNPP Rabi’u Kwankwaso, yace Gwamnatin da zata magance matsalar tsaro tare da inganta tattalin arziki idan aka zaɓe shi a matsayin Shugaban Ƙasa a Shekarar 2023.

Ya bayyana haka a ranar Litinin a Calabar a lokacin da yake jawabi ga Ɗumbin Magoya Bayan sa, bayan nasarar daya samu a Zaɓen Fidda Gwani.

“Matsalar tsaro da suka haɗa da Ta’addanci, da wasu matsalolin duk za’a magance su,” yana mai ƙara dacewa “zai inganta tattalin arzikin Kasa, kuma NNPP zata tabbatar da haɗin kan Ƙasa”.

Yace Jam’iyyar nada mutane masu daraja, da zasu iya jagorantar Ƙasar, sai ya buƙaci magoya bayan sa dasu samo Katin Ɗan Ƙasa domin Babban Zaɓen Shekara mai zuwa.

Yace Jam’iyyar ta zama Sananniya a dukkanin Ƙananan Hukumomi na Ƙasar.

Tunda Farko, Shugaban Jam’iyyar Tony Odey, ya bayyana Kwankwaso a matsayin wanda yazo domin ceto Ƴan Najeriya.

wt11 gif

Leave A Reply

Your email address will not be published.

This site uses Akismet to reduce spam. Learn how your comment data is processed.

This website uses cookies to improve your experience. We'll assume you're ok with this, but you can opt-out if you wish. Accept Read More

Privacy & Cookies Policy